Nigerian news All categories All tags
Kasuwanci: Jihar Kaduna ta samu lambar yabo daga Fadar Shugaban kasa

Kasuwanci: Jihar Kaduna ta samu lambar yabo daga Fadar Shugaban kasa

A ranar Juma'ar da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta yiwa gwamnatin jihar Kaduna jinjina tare da ba ta lambar yabo kan muhimmiyar rawa da ta taka wajen saukakawa tare da inganta harkokin kasuwanci a fadin kasar nan ta Najeriya.

Bayan tantancewar da gwamnatin tarayya ta gudanar, wannan sanarwa ta zo ne da sanadin Jumoke Oduwole, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin masana'antu da cinikayya wanda ya bayyana cewa, jihar Kaduna ta ciri tuta a fadin kasar nan wajen saukakawa tare da inganta harkokin kasuwanci.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i

A yayin ganawa da manema labarai a taron Bankin Duniya da aka gudanar domin nazari akan tsare-tsaren saukaka kasuwanci cikin jihohi 19 na Arewacin Najeriya, Oduwole ya yabawa kokarin gwamna Nasir El-Rufa'i wajen habaka tattalin arziki.

Yake cewa, wannan rawa da jihar Kaduna ke takawa wajen habakar tattalin arziki zai kara inganta matsayin kasar nan a Bankin Duniya kan harkokin kasuwanci.

KARANTA KUMA: Sauya Fasalin Zaben 2019: Sanatoci 42 na goyon bayan shugaba Buhari

A na sa jawabin mataimakin gwamnan jihar Barnabas Yusuf Bala ya bayyana cewa, wannan shiri da gwamnatin Kaduna ke aiwatar domin saukaka cinikayya yana daya daga cikin manufofin da ta kudiri aniyya wajen habaka tattalin arziki tare da kara karfin gwiwar kasuwanci a jihar.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne hukumar 'yan sanda ta kudiri aniyyar fara binciken miyagun makamai a gidajen mazauna babban birnin kasar nan na Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel