Nigerian news All categories All tags
Martani: Jam'iyyar PDP ta lissafa 'yan APC 50 da ta ce duk barayi ne

Martani: Jam'iyyar PDP ta lissafa 'yan APC 50 da ta ce duk barayi ne

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana jerin mutanen da gwamnatin APC ta wallafa da sunan cewa barayi ne a matsayin karya da soki-burutsu tsagwaron sa.

Haka zalika jam'iyyar ta PDP ta kuma bayyana cewa an zayyana sunayen wasu daga cikin jiga-jigan ta ne kawai domin a bata masu suna duk kuwa da cewa wasu daga cikin su duk maganar su na a gaban kotu.

Martani: Jam'iyyar PDP ta lissafa 'yan APC 50 da ta ce duk barayi ne

Martani: Jam'iyyar PDP ta lissafa 'yan APC 50 da ta ce duk barayi ne

KU KARANTA: Kisan Zamfara: Sarkin Anka ya bukaci agajin majalisar dinkin duniya

Wadanda jam'iyya ta lissafa dai sun hada da tsaffin gwamnoni da suka hada da Rotimi Amaechi, Timipre Sylva, Bukola Saraki, Rabiu Kwankwaso, Aliyu Wammako, Sullivan Chime, Orji Kalu, Ngige, Abdullahi Adamu.

Sauran sun hada da wasu gwamnonin da ke ci yanzu kamar Abubakar Moh’d, Gov. Lalong. Haka ma hadda wasu yan majalisar da suka hada da Bello Hayatu, Sen. Binta Massi.

Sauran sun hada da Mal. Nuhu Ribadu, Dr.Idi Hong, Adm. Murtala Nyako, Sen. AbdulAzeez Ibrahim, Sen. Adamu Aliero, George Akume, Sen. AbdulAzeez Nyako, Sen. Alkali Moh’d, Dr.Aliyu Modibbo, Sen. Silas Zwingima, Sen. Bello Tukur, Jummai Al-Hassan, Sen. Andy Uba, Sen. Nazif, Sen. Magnus Abe, Engr. Dakuku Peterside, Sen. Hunkuyi, Joshua Dariye.

Kamar dai yadda jadawalin ya kunsa, hadda tsaffin kakakin majalisar wakilai irin su Aminu Masari, Aminu Tambuwal, Yakubu Dogara, Gali Na’abba.

Sai kuma tsaffin shugabannin jam'iyyar ta PDP din kamar su Barnabas Gemade da Audu Ogbe.

Haka ma dai jadawili ya kuma kunshi sunayenDambazau, Oserheimen Osunbo, Musliu Obanikoro, Adam Oshiomhole, Abubakar Sani Bello, Ahmed of Kwara, Dakingari, Danjuma Goje, Obanikoro, Sen. Lokobiri Jim Nwobodo, Govs Atiku Bagudu, Ganduje, Nasir El-Rufai, Ortom, Ishaku Darius, Rochas Okorocha, Bindo Jibrilla, da kuma Chinweke Mbadinuju.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel