Nigerian news All categories All tags
Zamu fitar da sunayen barayin gwamnati da ke cikin APC - Jam'iyyar PDP

Zamu fitar da sunayen barayin gwamnati da ke cikin APC - Jam'iyyar PDP

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce nan bada dadewa ba zata fara tattara sunayen barayin dukiyar gwamnati da ke buya a jam'iyyar APC har ma da wadanda ke rike da mukamai a cikin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Yayin da ta ke mayar da martani a kan sunayen barayin gwamnati da gwamnatin tarayya ta fitar jiya, PDP ta ce abin dariyya da takaici kuma gwamnatin na Buhari ta tsokalo tsuliyar dodo kamar yadda kafar yadda labarai na The Cable ta ruwaito.

Zamu fitar da sunayen barayin gwamnati da ke cikin APC - Jam'iyyar PDP

Zamu fitar da sunayen barayin gwamnati da ke cikin APC - Jam'iyyar PDP

A dai jiya ne Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ya fitar da sunayen 'Barayin dukiyar gwamnati' a wata taron manema labarai da ya kira.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama bindigogi 35 da alburusai 222 a jihar Nasarawa

Amma a martanin da ya mayar, mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ya cacaki gwamnatin tarayyar inda ya zargi ta da cire sunayen yan jam'iyyar APC da ke fuskantar sharia'h kan tuhumar rashawa a kotunan kasar nan.

Ya kuma kara da cewa cikin dukkan mutanen da aka ambata babu wanda kotu ta tabbatar da cewa ya saci kudin gwamnati balle a kai ga yanke hukunci. Ya ce fitar da sunayen kawai farfaganda ce da bita-da-kulle.

Olognondiyan ya kuma ce "Babu shakka duk wadanda aka ambaci sunayen su za su tafi kotu don bin hakkin su. Wannan fa itace gwamnatin da ta kasa bayyana wa yan Najeriya yadda akayi $26bn ya bace a NNPC da kuma danyen mai na triliyan 1.1 da aka karkatar don amfani da shi a jam'iyyar APC da naira biliyan 18 da aka ware don yan gudun hijira amma APC ta sace. Naira biliyan 10 kuma ya bace a hukumar NHIS amma duk da haka gwamnatin Buhari ta mayar da shugaban hukumar kan kujerar mulkin sa."

Mai magana da yawun jam'iyyar na PDP ya ce wannan zargin da bashi da tushe ba zai hana PDP ta cigaba da kallubalantar APC ta cika wa al'umma alkwawuran da ta dauki lokacin yakin neman zabe ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel