Martanin Shehu Sani kan martanin Nasir ElRufai kan batun hanin majalisa na ciwo wa Kaduna bashi

Martanin Shehu Sani kan martanin Nasir ElRufai kan batun hanin majalisa na ciwo wa Kaduna bashi

- Ba'a ga-maciji tsakanin Shehu Sani da Elrufai

- Majalisa ta hana ciyo bashin, gwamnati tace munafukai suka janyo

- Sanatan yace ba don talaka za'a ciyo ba, cinye wa za'ayi

Martanin Shehu Sani kan martanin Nasir ElRufai kan batun hanin majalisa na ciwo wa Kaduna bashi

Martanin Shehu Sani kan martanin Nasir ElRufai kan batun hanin majalisa na ciwo wa Kaduna bashi

Yinin yau kaf, Sanatan Kaduna yana ta kokarin kare kansa a shafukan sada zumunta kan cewar gwamnati wai shi yayi kutun-kutun ya hana a ciyo bashi don manyan ayyuka a jihar Kaduna wanda majalisar dattijai tay fatali dashi.

A cewar dattijion sanatan dai, bashin ba don ayyuka za'a ciyo shi ba, a'a sai don a ci gaba da gallazawa 'yan hamayya, da ma kuma siyasar 2019.

Sanatan ya kara da cewa, talakawa yayi wa wannan kokari, domin su da 'ya'yansu za'a bari da bashi, su kuma wadanda ke mulki, zasu arzurta kansu da 'ya'yansu.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya yabi Buhari kan batun ilimi

Ga dukkan alamu dai, jam'iyyar APC ta jihar, zata nemi daukar mataki kan Sanatan musamman idan gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya so hakan.

Daga cikin abin da yaka iya rasawa, shine kujerarsa ta takarar firamare a cikin gidan APC, inda watakil su sanya Uba Sani ya kayar dashi.

PDP dai da SDP sun zamm gidaje da zawarawa ka iya shiga domin su sami damar ramako, muddin aka koro mutane a zabukan 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel