Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Jami’an yan sanda sun damke 5 cikin 6 da suka tsere daga kurkukun yan sandan a Kogi

Yanzu-yanzu: Jami’an yan sanda sun damke 5 cikin 6 da suka tsere daga kurkukun yan sandan a Kogi

Hukumar yan sandan Najeriya ta damke guda 5 cikin 6 na yan barandan da suka tsere daga kurkukun hukumar a garin Lokoja, babba birnin jihar Kogi ranan Laraba.

Yan barandan na da alaka da sanata mai wakiltan Kogi ta yamma, Dino Melaye.

Jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa masu garkuwa da mutane kuma yan bindiga dadin ke ake damke kwanakin baya da suka bayyana cewa sanata Dino Melaye suke wa aiki sun arce daga kurkukun yan sanda.

A wannan karon, yan bindigan sun balle kurkukun jami’an yan sandan SARS da ke garin Lokoja, jihar Kogi tare da wasu da ke kurkukun can dama.

Yanzu-yanzu: Jami’an yan sanda sun damke 5 cikin 6 da suka tsere daga kurkukun yan sandan a Kogi

Yanzu-yanzu: Jami’an yan sanda sun damke 5 cikin 6 da suka tsere daga kurkukun yan sandan a Kogi

Hukumar yan sandan Najeriya a ta damke yan daba 2 wadanda ke yiwa sanata mai wakiltan mazabar Kogi ta yamma a majalisan dattawa, Dino Melaye, domin kawo rikici lokacin zaben 2019.

KU KARANTA: Yan barandan da ke yiwa Melaye aiki sun tsere

Kakakin hukumar yan sandan, Jimoh Moshood, ya bayyana yan barandan masu suna Kabiru Saidu wanda akafi sani da Osama da Nuhu Salish, da jami’an SARS suka damke a jihar Kogi ranan 19 ga watan Junairu 2018 a Ogujeje, karamar hukumar Dekina na jihar Kogi.

Ya ce yan barandan sun bayyana da bakunansu cewa su mambobin wata kungiyar masu garkuwa da mutane ne kuma sunawa yan siyasa banga a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel