Nigerian news All categories All tags
Sakin sunayen barayin gwamnati: Cikin ushi PDP ta mayar wa da APC martani kan satar kudin da aka tafka a mulkinta

Sakin sunayen barayin gwamnati: Cikin ushi PDP ta mayar wa da APC martani kan satar kudin da aka tafka a mulkinta

- An saki sunayen wadanda suka saci kudin makamai a dazu

- Dukkaninsu hadiman tsohon shugaba Jonathan ne

- PDP ta ce ai ba ita kadai ce barauniya ba

Sakin sunayen barayin gwamnati: Cikin ushi PDP ta mayar wa da APC martani kan satar kudin da aka tafka a mulkinta

Sakin sunayen barayin gwamnati: Cikin ushi PDP ta mayar wa da APC martani kan satar kudin da aka tafka a mulkinta

Cece-kuce sai barkowa yake daga bangarorin siyasar kasar nan tun bayan da gwamnatin APC ta saki sunayen barayin gwamnati da aka kama dumu-dumu da kudaden sata a lokacin mulkin PDP. Laifuka da har yanzu ana ta jansu a kotu saboda lauyoyi sun sha kudi.

Martanin PDP yazo cikin fushi, ta bakin Kola Ologbondiyan National Publicity Secretary na jam'iyyar mai adawa, mai kuma neman lallai sai APC ta janye kalamanta wanda tace sun bata masa suna, gabanin zaben 2019.

A baya dai PDP din ta mulki kasar nan shekaru 16, kuma a zamaninsu an tafka sata mai bala'in yawa.

A cewar sakataren na PDP dai, sai dai gwamnatin ta APC ta saki sunaye harda na 'barayin APC domin suma sun kwasa.

DUBA WANNAN: Aikin majalisar dattijai a shekara biyu ya zarta na kowanne tun 1999

Cikin fushi ya kara da cewa, ai dukkan wadanda aka saki sunayen nasu iyalai da hadiman tsohon shugaba Jonathan ne.

Ya kuma kara da cewa, duk abin da kotu bata tabbatar ba ai bata suna ne ace laifi aka yi.

Gabanin zabukan 2019 dai, muhawara na kara zafi, adawa na kara zafi, talakka kuma ake so sai lallai ya rufe ido ya sake zabo baragurbi daga kowacce jam'iyya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel