Nigerian news All categories All tags
Muhimman bayanai 5 da Shugaba Buhari yayi a cikin jawabin sa na Esta ga Kiristocin Najeriya

Muhimman bayanai 5 da Shugaba Buhari yayi a cikin jawabin sa na Esta ga Kiristocin Najeriya

Yau dai kamar yadda aka sani ita ce ranar bukukuwan Esta ga al'ummar duniya baki daya da ke bin addinin Kirista.

Haka ma dai yau ranar hutu ce a Najeriya domin bada dama ga mabiya addinin Kiristan da su yi ibadar su.

Ga kadan daga cikin muhimman batutuwan da shugaba Buhari ya fada a cikin sakon taya murna ga al'ummar kirista na Najeriya din:

Muhimman bayanai 5 da Shugaba Buhari yayi a cikin jawabin sa na Esta ga Kiristocin Najeriya

Muhimman bayanai 5 da Shugaba Buhari yayi a cikin jawabin sa na Esta ga Kiristocin Najeriya

KU KARANTA: An gano wanda ya watsawa dalibar jami'ar Maiduguri ruwan guba

1. Shugaban kasar ya godewa Allah da ya ba mu tsawon rai wajen ganin wata shekarar tare da kuma ganin zagayowar ranar.

2. Shugaban kasar haka zalika yayi kira ga dukkan 'yan Najeriya da su kaunaci juna sannan kuma su saka halayen yafiya da kishin kasa tare da tsoron Allah a zukatan su.

3. Shugaba Muhammadu Buhari kuma ya garggadi 'yan Najeriya game da furta kalaman batanci da kuma tunzura jama'a.

4. Haka ma Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da wadanda ya kira masu kokarin yin anfani da halin tabarbarewar tsaron kasar nan wajen yin siyasa.

5. Haka ma Shugaba Muhammadu Buhari yayi alkawarin yin duk abunda ya wajaba wajen ganin ya maido sauran 'yan matan Chibok da ma dayar dalibar Dapchi da ke a hannun 'yan ta'adda.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel