Nigerian news All categories All tags
'Matsayar gwamnatin Kaduna kan hanin ciwo bashi da majalisar dattijai tayi'

'Matsayar gwamnatin Kaduna kan hanin ciwo bashi da majalisar dattijai tayi'

- Gwamnatin ta ta'allaka rashin samun goyon bayan ga 'munauncin Shehu Sani

- Tace dama kudin don talakawa zata ciyo su

- Wasu na ganin kudin don zabe za'a amso su

'Matsayar gwamnatin Kaduna kan hanin ciwo bashi da majalisar dattijai tayi'

'Matsayar gwamnatin Kaduna kan hanin ciwo bashi da majalisar dattijai tayi'

A ta bakin Samuel Aruwan, kakakin gwamnatin jihar ta Kaduna, kudaden dama an so ciyo bashinsu ne, wadanda tuni bankunan kasar wajen sun amince a ciyo su, amma majalisa ta hana, kudaden da sun kai akalla dala miliyan 300, kusan biliyan daya.

Su dai bangaren su Sanata Shehu Sani, sun cije kan lallai kar a samo kudin, domin a cewarsu, siyasa za'a yi da kudin ba wai aiki ga talakawa ko daukar malamai ba.

A cewar hadimin gwamna Elrufai, Mukhtar Garba Maigamo, a shafinsa na yanar gizo, gwamnatinsu tuni dama ta ci karfin ayyukan da ta sanya a gaba da kusan kashi 70 cikin dari, domin sun sa rai dama sanatan zayyi duk yadda zayyi ya kassara siyasar jihar tasa da talakawanta.

DUBA WANNAN: Ajaokuta ta sami tagomashi daga Tarayya

Majalisa ce kadai ke da damar sahalewa jihohi ciwo bashi daga kasar waje, musamman makudan daloli, kuma ya zuwa yanzu, Kaduna, Edo da Legas ce ke niyya ko amso bashin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel