Nigerian news All categories All tags
Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC

Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwa ye ba sun farwa wani babban jigon jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress ta jihar Edo dake a shiyyar kudu maso kudancin kasar nan, mai suna Mista Samson Sedi a karamar hukumarEtsako ta yamma.

Haka zalika kamar dai yadda muka samu, kwamishinan 'yan sandan jihar ta Edo Mista Johnson Kokumo ma ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mamacin ya mutu ne bayan an garzaya da shi asibiti.

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe wani babban jigon jam'iyyar APC

KU KARANTA: Yan Najeriya sun yafe mana - PDP

Legit.ng ta samu cewa sai dai Mista Johnson Kokumo ya kara jaddada cewa tuni jami'an sa suka dukufa wajen ganin sun cafke wanda yayi ta'asar.

A wani labarin kuma, Wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton makiyaya ne a ranar Alhamis din da ta gabata a lokuta daban daban sun farwa wasu kauyukan da suka hada da Baking Kofi da kuma Kaninkon dukkan su a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna inda kuma suka kashe mutum shidda tare da jikkata wasu hudu.

Kamar yadda muka samu, 'yan bindigar da majiyar mu ta bayyana cewa sun kai su 10 sanye da kayan sojoji ne dai suka farma kauyukan tare da yin wannan danyen aika-aika da tsakar dare.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel