Nigerian news All categories All tags
Tuni 'yan Najeriya suka yafe mana dukkan zunuban mu - Jam'iyyar PDP

Tuni 'yan Najeriya suka yafe mana dukkan zunuban mu - Jam'iyyar PDP

Madugun jam'iyyun adawa a Najeriya watau jam'iyyar PDP ta bayyana cewa tuni ta gane cewa daukacin al'ummar Najeriya sun riga sun yafe masu dukkan kurakuran da suka tafka biyo bayan neman gafararsu da suka yi

Babban jami'in hulda da ama'a na jam'iyyar ta PDP a mataki na tarayya watau Mista Kola Ologbondiyan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun sa da ya fitar.

Tuni 'yan Najeriya suka yafe mana dukkan zunuban mu - Jam'iyyar PDP

Tuni 'yan Najeriya suka yafe mana dukkan zunuban mu - Jam'iyyar PDP

KU KARANTA: Aina'u Ade ta ayyana lokacin auren ta

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Mista Kola Ologbondiyan ya kuma bayyana cewa jam'iyyar ta yanke shawarar neman gafarar ce saboda kishin kasa da kuma zimmar samar da hadin kai da farfado da martabar Nijeriya.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya da ke da alhakin kula da harkokin aikin hajji watau National Hajj Commission of Nigeria (NAHCON) a turance ta sanar da kara wa'adin yin rijista ga maniyyata aikin hajjin na bana shekarar 2018 ya zuwa karshen watan Afrilu mai zuwa.

Wannan dai kamar yadda muka samu na kunshe ne a cikin wata takardar manema labarai dauke da sa hannun jami'ar hulda da jama'a ta hukumar ta fitar mai suna Hajiya Fatima Mustapha Muhammad.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel