Hutu da gwamnatin Legas ta bayar: A cewar masana, ziyarar Buhari zuwa Ikko ta kawo tsaiko da cinkoso da ya jawo asarar N1b da doriya

Hutu da gwamnatin Legas ta bayar: A cewar masana, ziyarar Buhari zuwa Ikko ta kawo tsaiko da cinkoso da ya jawo asarar N1b da doriya

- Ziyarar Lagos da Buhari yayi ta tsayar da birnin Lagos awa 24

- MAsu kiyasi sunce aqn yi asarar Naira bliyan daya saboda ba'a yi aiki ba

- Jihar Lagos dai hutu ta bayar don ziyarar tayi armashi

Hutu da gwamnatin Legas ta bayar: A cewar masana, ziyarar Buhari zuwa Ikko ta kawo tsaiko da cinkoso da ya jawo asarar N1b da doriya
Hutu da gwamnatin Legas ta bayar: A cewar masana, ziyarar Buhari zuwa Ikko ta kawo tsaiko da cinkoso da ya jawo asarar N1b da doriya

Masu hada-hada da kasuwanci, da kididdiga a jihar Lagos, wadanda ake kira ProShare, sun yi kiyasin nawa aka yi asara a jihar a jiya, bayan da ziyarar shugaba Buhari ta tsayar da birnin chak, inda gwamnatin jihar ta bada hutu.

A cewarsu dai, jihar ta yi asarar kudaden shiga, haraji, da ma na zirga zirga da suka kai akalla N1,250,000,000, wanda ya kamata ace an kashe ko an yi musaya a kasuwanni, amma ba'a yi ba.

Wannan yazo ne saboda kasuwanni, tituna, jirage da ma tituna duk sun rue babu wanda yayi aiki a jiyan, saboda shugaban na shawagi a titunan jihar domin kaddamar da manyan ayyuka da jihar tayi.

DUBA WANNAN: KAmfanin Tecno zai komo aiki Najeriya saboda nan ribar take

A dalilinsu dai na bada hutun, gwamnati rufe tituna manya domin baiwa shugaban damar zagayawa cikin sauri da ma kara wa masu tsarn lafiyarsa karfi da karsashi yayin kula da cunkoso.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel