Nigerian news All categories All tags
Rikicin siyasar Gwamna El-Rufai da Sanatocin Kaduna ya ja an hana Kaduna aron kudi

Rikicin siyasar Gwamna El-Rufai da Sanatocin Kaduna ya ja an hana Kaduna aron kudi

Kun samu labari cewa a makon nan ne Majalisar Dattawa ta hana Jihar Kaduna karbo bashin da tayi niyya bayan sama da shekara guda kokon Jihar na yawo a Majalisa. Gwamna Nasir El-Rufai dai yace aiki za ayi wa al’ummar Kaduna da wannan kudin.

Rikicin siyasar Gwamna El-Rufai da Sanatocin Kaduna ya ja an hana Kaduna aron kudi

Sulaiman Hunkuyi APC da Danjuma Laah PDP ba su yarda Kaduna ta ci bashi ba

Sanatan yace kwamitin sa ta zauna ta duba kuma ta gano cewa bai dace a ba Jihar Kaduna damar cin wannan bashi ba saboda Jihar za ta zama ta biyu wajen yawan bashi a Kasar. Legas ce kurum za ta zama a gaban Kaduna idan aka karbo wannan bashi.

KU KARANTA: An hana Gwamnatin Jihar Kaduna cin bashi daga kasar waje

A lokacin da Sanatan ya bayyanawa Majalisa abin da kwamitin sa su kayi, sauran Sanatocin Kaduna sun nemi a hana Gwamnan Jihar karbar wannan bashi. Ike Ekweremadu ya nemi jin ta bakin sauran Sanatocin wanda da dama su kayi na’am da hakan.

Dama can Gwamnan ba ya shiri da Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani yayin da kuma cikin ‘yan kwanakin nan ya rusa gidan Sanata Sulaiman Hunkuyi. Shi ma da Sanatan Kudancin Kaduna Danjuma Laah na Jam’iyyar PDP ba su tare da Gwamnan Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel