Bazamu daina maganar rashawa da cin hanci da PDP tayi ba - APC

Bazamu daina maganar rashawa da cin hanci da PDP tayi ba - APC

- Shugaba Muhammadu Buhari yace Asiwaju abokin siyasarsa ne

- Tinubu ya bukaci ‘Yan Najeriya da kada su amince da hakurin da PDP ta bayar

- PDP sun fadawa Tinubu cewa kada ya kara yaudarar kansa

A jiyane wurin taron da aka gabatar a jihar Legas, abokai da aminnan arziiki na tsohon gwamnan jihar Legas kuma shugaban jam’iyyar APC na tarayya, Asiwaju Bola Tinubu, tare da jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, suka bayyana cewa bazasu daina maganar rashawa da cin hanci da akayi a gwamnatin Goodluck Jonathan ba.

A taron na 10 wanda akayi na bikin cikar Tinubu shekaru 66, a Eko Hotel, ya samu halartan manya ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sai Gwamnoni 11, sai Ministoci, sai kuma shuwagabannin jam’iyyar APC duk sun halarci wurin.

Bazamu daina maganar rashawa da cin hanci da PDP tayi ba - APC

Bazamu daina maganar rashawa da cin hanci da PDP tayi ba - APC

Kungiyar ‘yan kasuwa wanda Alhaji Aliko Dangote, Mista Jim Ovia, da Dr. Oba Otudeko suka wakilta.

Wadanda ake tsammanin basu samu halarta ba sune jami’an majalisa dattawa, da kuma Ciyaman na jami’yyar APC, Chief John Odigie-Oyegun.

Taron wanda tsofaffin abokan aikinsa ne lokacin da yake aiki jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007, suka hada masa bukin a don tinawa da ayyukan cigaba da yayi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Sakon shugaba Buhari game da bikin Easter

Taron anyi amfani dashi ne an nuna cigaban da gwamnatin Buhari ta kawo; kamarsu ciyar da yara ‘yan makarata abinci da kuma N-power wanda ake amfani da matasa marsa aikinyi wurin gudanar da ayyuka ana biyansu duk wata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel