Zargin makamai: Dino Melaye ya taso Shugaban ‘Yan Sanda a gaba

Zargin makamai: Dino Melaye ya taso Shugaban ‘Yan Sanda a gaba

- Sanata Dino Melaye yayi barazanar maka Sufetan ‘Yan Sanda a Kotu

- Ana dai zargin ‘Dan Majalisar Dattawan da ba wasu mutane makamai

- Sanatan ya nemi a fito da wadanda ake zargin sa da rabawa makaman

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust ta kasar nan cewa ‘Dan Majalisar Dattawan da ke wakiltar Yammacin Jihar Kogi watau Dino Melaye ya taso rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a gaba inda yayi barazanar shiga Kotu domin shari’a.

Zargin makamai: Dino Melaye ya taso Shugaban ‘Yan Sanda a gaba

Sanata Dino Melaye na shirin shiga Kotu da IGP

Sanatan ya hurowa ‘Yan Sandan Najeriya wuta ne game da zargin da ke kan sa na ba wasu tsageru makamai. Kwanaki aka kama wadanda ake zargi Sanatan ya rabawa makamai sai kuma kurum aka ji cewa sun tsere daga hannun ‘Yan Sandan.

KU KARANTA: An birne wasu Sojojin Najeriya 11 a Garin Kaduna

Fitaccen ‘Dan Majalisar Dino Melaye ya bayyana cewa zai iya shiga Kotu da IG Sufetan ‘Yan Sandan kasar Ibrahim K. Idris idan aka gagara kamo wadanda ake zargin sa da ba su makamai. Melaye zai kai kara a Kotu domin a fitar masa da hakkin sa.

Dino Melaye ya tabbatar da cewa ba buya yake yi ba kamar yadda ake ta rayawa inda ma yayi barazanar shiga kotu domin yayi shari’a da ‘Yan Sandan kasar idan ba a kamo mutane 6 da aka ce sun tsere ba. Sanatan yace a fito da su ko a raye ko a mace.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel