Nigerian news All categories All tags
An yanka ta tashi: An hana Gwamnatin Jihar Kaduna karbo bashin kudi daga kasar waje

An yanka ta tashi: An hana Gwamnatin Jihar Kaduna karbo bashin kudi daga kasar waje

- Kaduna ba za ta karbo bashin Dala Miliyan 350 daga kasar waje ba

- Majalisar Dattawa tace bashin yayi yawa saboda ba za ta yarda ba

- Sanatocin Kaduna duk sun yi na’am da wannan mataki da aka dauka

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust Majalisar Dattawa ta hana Gwamnatin Jihar Kaduna karbo bashin makudan miliyoyin kudin da tayi niyya daga kasar waje. Kudin da ake neman cin bashin sun kai Dala Miliyan 350.

Sanatocin sun takawa Gwamnan Kaduna burki sun hana shi cin bashi daga kasar waje

An hana El-Rufai karbo bashin miliyoyin Daloli daga kasar waje

Bayan fiye da shekara guda da mika mata kokon bara, Majalisar Dattawa tayi watsi da maganar cin bashin da Jihar Kaduna ke shirin yi. Shugaban kwamitin da ke lura da bashin gida da waje watau Shehu Sani ya bayyana wannan.

KU KARANTA: 'Yan Sanda za su fara binciken gidaje a Jihar Kaduna

Sanata Shehu Sani yace idan har aka bada damar karbo wannan bashi, kudin da ake bin Jihar Kaduna zai karu kwarai da gaske kuma Jihar Kaduna za ta zama ta biyu a wajen yawan bashi a kaf Najeriya wanda kuma babban hadari ne.

Wani Sanata na Jihar Kaduna Sulaiman Othman Hunkuyi yayi na’am da hana bada wannan bashi inda yace ba abin da ya dace Gwamnatin tayi ba kenan. Shi ma wani Sanatan da ke wakiltar Jihar Kaduna Danjuma Laah yace hakan yayi daidai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel