Ya bankawa kyakykyawar budurwar kaninsa wuta saboda taki amincewa da shi

Ya bankawa kyakykyawar budurwar kaninsa wuta saboda taki amincewa da shi

- Wata budurwa, Ebor Lovina, ta mutu bayan yayan saurayinta ya cinna mata wuta saboda taki amincewa ya yi lalata da ita

- Lovina ta mutu ne bayan an garzaya da ita asibiti domin ceto rayuwar ta

- Rahotanni sun bayyana cewar Lovina ta kammala karatun digiri a jami'ar Ambrose Ali kuma tana aiki a Sun-Ray Hotel

Wata budurwa, Ebor Lovina, ta rasa ranta yayin kokarin kare mutuncinta da kare hakkin soyayyar dake tsakaninta da saurayinta.

Sai dai kokarin Lovina na kare mutuncinta ya jawo mata asarar ranta ta hanya mai matukar ciwo da tayar da hankali.

Ya bankawa kyakykyawar budurwar kaninsa wuta saboda taki amincewa da shi

Ya bankawa kyakykyawar budurwar kaninsa wuta saboda taki amincewa da shi

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojoji 11 da aka binne yau a Kaduna

Kamar yadda wasu abokan Lovina suka bayyana a dandalin sada zumunta na Facebook, sun ce, yayan saurayin Lovina ya cinna mata wuta saboda taki amincewa ya yi lalata da ita.

Lamarin ya faru ne a garin Benin, jihar Edo. An garzaya da Lovina asibiti domin ceto rayuwar ta amma saidai hakan bai yiwu ba, domin ta mutu jim kadan bayan kaita asibitin.

Kyakykyawar budurwar ta kammala karatunta na digiri a jami'ar Ambrose Ali dake Ekpoma a jihar Edo, kuma tana aiki a Otal din Sun-Ray dake birnin Benin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel