Nigerian news All categories All tags
Wani Jigo a APC ya ba Oyegun shawara ya tattara ya koma gona

Wani Jigo a APC ya ba Oyegun shawara ya tattara ya koma gona

- Mr. Timi Frank yayi murna da matakin da Shugaban kasa ya dauka a APC

- Jigo a Jam’iyyar yace ya kamata John Odigie Oyegun ya hakura da siyasa

- Shugaba Buhari bai yi na’am da karawa Shugabannin Jam’iyyar wa’adi ba

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Kwamared Timi Frank wanda yana cikin manyan Jam’iyyar APC yayi kaca-kaca da Shugaban Jam’iyyar John Odigie-Oyegun inda yace tun farko ya kamata a sauke sa.

Wani Jigo a APC ya ba Oyegun shawara ya tattara ya koma gona

Frank yace ya kamata Oyegun ya hakura da harkar siyasa

Mataimakin Sakataren yada labarai na Jam’iyyar mai mulki Timi Frank yayi kira ga Shugaban Jam’iyyar APC John Oyegun ya tattara ya bar kujerar sa. Frank yace Oyegun ya hakura da siyasa ya koma harkar noma.

KU KARANTA: Jigon APC Bola Tinubu yayi kaca-kaca da Jam'iyyar PDP

Timi Frank ya fitar da jawabi ne a Abuja inda ya nemi Shugaban Jam’iyyar na kasa ya koma kauyen sa don siyasa ba na shi bane. Frank ya kuma soki Majalisar NWC bisa kalaman da tayi kan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sakataren yada labaran na APC yace Jam’iyyar APC ta gaza yin wani abin kirki a karkashin John Oyegun da Majalisar ta. Frank ya yabawa matakin da Shugaban kasar ya dauka game da wa’adin Shugabannin Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel