Nigerian news All categories All tags
Kungiyar ‘Yan Arewa ta ware kanta daga cikin masu jefa kuri’ar rashin tabbashi ga Buhari

Kungiyar ‘Yan Arewa ta ware kanta daga cikin masu jefa kuri’ar rashin tabbashi ga Buhari

- Kungiyar Arewa Consultative Forum ta ware kanta daga masu nuna rashin tabbashi ga sugaba Muhammadu Buhar da sauran ‘yan siyasar Arewa

- Babban jagoran kungiyar ta Dattawan Arewa, Prof. Ango Abadullahi da wasu kungiyoyi 17 sun jefa kuri’ar rashin tabbashi ga shugaba Buhari

- Abdullahi wanda tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello ne a Zaria, shine makasudin taron da aka gabatar a Arewa House, jihar Kaduna

Kungiyar Arewa Consultative Forum ta ware kanta daga masu nuna rashin tabbashi ga sugaba Muhammadu Buhar da sauran ‘yan siyasar Arewa.

Babban jagoran kungiyar ta Dattawan Arewa, Prof. Ango Abadullahi da wasu kungiyoyi 17 sun jefa kuri’ar rashin tabbashi ga shugaba Buhari, sun bayyana hakan ne a ranar Asabar 24 ga watan Maris, shekarar 2018, sunce shugaban kasar ya kasawa ‘Yan Arewa.

Abdullahi wanda tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello ne a Zaria, shine makasudin taron da aka gabatar a Arewa House, jihar Kaduna. Kungiyar ta bayyana cewa tana kokarin neman dan “takara na kirki” wanda zai maye gurbin shugaban kasar.

Kungiyar ‘Yan Arewa ta ware kanta daga cikin masu jefa kuri’ar rashin tabbashi ga Buhari

Kungiyar ‘Yan Arewa ta ware kanta daga cikin masu jefa kuri’ar rashin tabbashi ga Buhari

Amma a ranar Alhamis ne kungiyar, ta kebe kanta daga cikin masu jefa kuri’ar rashin tabbashi ga Buhari da’yan siyasa na yankin arewa.

KU KARANTA KUMA: Hukumar ‘Yan Sanda a jihar Edo ta kama wasu mutane 5 da makamai 120

Sakataren kungiyar na tarayya Muhammad Biu, a jawabinsa yace har yanzu kungiyar bata yanke shawara akan shugaban kasar ba, yace idan lokaci yayi kungiyar ta Arewa zata bayyanawa ‘Yan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel