An nemi masoyan Shugaba Buhari su lissafo aikin da Gwamnatin nan ta iya kammalawa cikin shekaru 3

An nemi masoyan Shugaba Buhari su lissafo aikin da Gwamnatin nan ta iya kammalawa cikin shekaru 3

- Wani Bawan Allah ya sa kudi ga wanda ya kawo masa ayyukan Buhari

- Yace duk wanda ya lissafo masa kwangilolin Buhari zai ba shi N20, 000

- Kusan dai an rasa wanda zai iya kawo masa ayyukan da aka kammala

A jiya ne wani Bawan Allah ya kalubalanci magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar nan su bayyana ayyukan da Gwamnatin Buhari ta iya kammalawa cikin shekara 3 da tayi tana mulki.

An nemi masoyan Shugaba Buhari su lissafo aikin da Gwamnatin nan ta iya kammalawa cikin shekaru 3

An sa kudi ga wanda ya jero ayyukan Gwamnatin Buhari

Oke Umurhowo a shafin sa na Tuwita ya sa tukwuicin kudi har N20, 000 ga wanda ya iya zayyano kwangilolin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta fara ta kammala. Daga baya dai an yi ta kara kudin har zuwa N70, 000.

KU KARANTA: An damfari Shugaban kasar Najeriya Buhari da lambar yabon karya

Jama’a da dama sun yi kokarin kawo ayyuka da dama da Gwamnatin nan tayi, sai dai wasu sun bayyana cewa ayyukan da dama da ake kira ba wannan Gwamnatin ce ta Shugaba Muhammadu Buhari ta fara su ta kammala ba.

Wani Bawan Allah mai suna Ibrahim Dalibi ya maida martani inda yace a Gwamnatin Buhari aka kamalla gine-ginen barikin Sojojin saman kasar a Garin Owerri da Katsina da sauran su ban da kayan aiki da aka saya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel