Nigerian news All categories All tags
Ku dawo da kudin da ku ka karba ba bisa ka'ida ba tunda an sanar da alawus din ku - SERAP ta fadawa 'yan majalisar dattijai

Ku dawo da kudin da ku ka karba ba bisa ka'ida ba tunda an sanar da alawus din ku - SERAP ta fadawa 'yan majalisar dattijai

Wata kungiya mai zaman kanta dake rajin rajin yaki da cin hanci da kuma tafiyar da mulki bisa gaskiya (SERAP) ta bukaci 'yan majalisar dattijai da su dawo da kudin da suka karba ba bisa ka'ida ba.

A wani jawabi da mataimakin darektan kungiyar, Timothy Adewale, ya fitar, kungiyar ta bukaci shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da takwaransa na majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da su tursasa mambobin majalisun tarayya da su dawo da kudaden da suka karba tunda ta bayyana cewar kudin da suka karba ya sabawa ka'ida.

Ku dawo da kudin da ku ka karba ba bisa ka'ida ba tunda an sanar da alawus din ku - SERAP ta fadawa 'yan majalisar dattijai

Majalisar dattijai

A kwanakin baya ne Sanatan Najeriya, Shehu Sani, ya bayyana cewar 'yan majalisar dattijai na karbar alawus din miliyan N13.5 duk wata a matsayin kudin gudanarwa.

Saidai, a ranar Litinin, hukumar kididdigar albashi da rabon kudin haraji ta kasa (RMAFC) ta bayyana cewar, kundin tsarin mulki ya yarda da biyan miliyan N1.36m ne ba miliyan N13.5m da suke karba ba.

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya ceci jam'iyyar APC - Shugaban jam'iyyar

Kakakin hukumar RMAFC, Ibrahim Mohammed, ya ce hukumar kula 'yan majalisu ce zata iya bayanin yadda aka yi 'yan majalisar suka mayar da alawus din fiye da abin da kundin tsarin mulki ya ayyana masu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel