Ba zamu taba mantawa da badakalar cin hanci da rashawa da ya gudana a zamanin Goodluck ba – Osinbajo

Ba zamu taba mantawa da badakalar cin hanci da rashawa da ya gudana a zamanin Goodluck ba – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewar ya zama wajibi ga gwamnati ta dinga tuna baya don kada a manta da badakalolin satar kudaden Najeriya da suka gudana a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Osinbajo ya bayyana haka ne a yayin bikin cika shekara 66 da haihuwa, na jagoran jam’iyyar APC, kuma Maigidansa, tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu da ya gudana a jihar Legas.

KU KARANTA: Shugaban Kiristocin Duniya Fafaroma ya karyata samuwar wutar Azaba a lahira

The Nation ta ruwaito Osinbajo yana fadin akwai bukatar a cigaba da tuna ma jama’a halin da aka shiga a gwamnatin Jonathan, musamman ta bangaren cin hanci da rashawa, don gane dalilin shigar Najeriya halin karayar tattalin arziki a farkon mulkin shugaba Buhari.

"Najeriya ta tsinci kanta ne a cikin wannan hali sakamakon sace sacen kudin gwamnati da ya gudana a gwamnatin data shude, don haka ya zama wajibi mu cigaba da tattauna wannan batu, don kada mu sake bin wannan turbar.” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Osinbajo ya amsa cewar har yanzu ba’a kai ga gaci ba a Najeriya, kamar yadda APC ta alkawarta, amma ya tabbatar da cewa gwamnatin Buhari ta daura kasar akan turbar samun cigaba mai daurewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel