Kun sata, kun lalata kudin Najeriya - Tinubu ya mayarwa da PDP martani

Kun sata, kun lalata kudin Najeriya - Tinubu ya mayarwa da PDP martani

Jagoran jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce, bai kamata jam'iyyar PDP take kokarin musanta cewar tayi almubazzaranci da salwantar da kudin Najeriya ba.

Tinubu na wannan kalamai ne a yau, Alhamis, a Legas, yayin wani taro da aka shirya domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar sa.

A kwanakin baya ne jam'iyyar PDP ta bakin kakakinta, Kola Ologbondiyan, ta ce bata saci kudin Najeriya ba tare da bayyana cewar shugaba Buhari ne yafi kowa cin moriyar badakalar da gwamnonin jam'iyyar PDP suka tafka sannan suka canja sheka zuwa jam'iyyar APC.

Kun sata, kun lalata kudin Najeriya - Tinubu ya mayarwa da PDP martani

Tinubu

Kazalika jam'iyyar ta PDP ta soki yaki da cin hanci da gwamnatin APC ke yi tunda ta kasa kama tsofin gwamnonin PDP da yanzu ke cikin APC.

DUBA WANNAN: A kalla mutane 70 sun hallaka sakamakon tashin wata gobara a gidan yari

Jam'iyyar ta PDP na yin wadannan kalamai ne bayan sukar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a kan biliyoyin da Jonathan ya kashe daga asusun gwamnatin Najeriya domin cin zaben 2015.

Kazalika, Osinbajo, ya tona asirin badakalar biliyoyin kudi da aka yi a kamfanin man fetur na kasa (NNPC). Zargin da jam'iyyar ta PDP ta sha musantawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel