Nigerian news All categories All tags
An bude duka hanyoyin jihar Legas duk da zuwan Shugaban kasa - Yan sanda

An bude duka hanyoyin jihar Legas duk da zuwan Shugaban kasa - Yan sanda

- Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Legas, Edgal Imohimi, ya tabbatarwa mutanen jihar cewa duk hanyoyi a bude suke don zirga-zirga

- Jawabin ya biyo bayan zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari na farko a jihar tun hawansa mulki

- Imohi ya tabbatarwa mutanen jihar cewa akwai kyakkyawan tsaro da kuma cewa hanyoyi na zirga-zirga a bude suke har tafiyar shugaban kasa

Hukumar ‘Yan Sanda ta jihar Legas yace, duk hanyoyin gari a bude suke don gudanar da al’amuran yau da kullun, duk da cewa shugaban kasa ya kai ziyara a jihar, kuma Eko Hall, ya dauki harami da manyan mutanen kasar nan masu jiran karasowar shugaban kasaMuhammadu Buhari, daga jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Edgal Imohimi, ya bayyana haka a ranar Alhamis, 29 ga watan Maris.

Wannan ziyarar mutane dayawa suna kallonta a matsayin ranar tarihi, saboda yau shekaru uku kenan da shugaban kasar, ya hau mulki amma bai taba kai ziyara jihar ta Legas ba sai wannan karon.

An bude duka hanyoyin jihar Legas duk da zuwan Shugaban kasa - Yan sanda

An bude duka hanyoyin jihar Legas duk da zuwan Shugaban kasa - Yan sanda

Shugaban kasar zaiyi ziyarar kwana biyu a jiyar ta Legas a ranar Alhamis, 29 ga watan Maris da Juma’a 30 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Tsohuwa mai shekara 100 ta musulunta a Abuja

Legit.ng ta ruwaito a baya cewa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 29 ga watan maris, a ziyararsa ta kwanaki biyu a jihar, zai kaddamar da babbar tashar motocin haya ta Ikeja, wadda gwamnatin jihar ta gina.

Tashar tana daya daga cikin ayyukan jihar na kokarin fadada garin. Tashar mai fadin 10,000 square metres, an cikata da kayayyakin aiki na zamani (ITS), ga na’ura mai bayar da sanyi an sanya a ko ina, ga ban dakuna, ga shaguna, ga wuraren abinci, ga injinan cire kudi na ATM, ga hanyar shiga yanar gizo kyauta, ga rumfuna masu amfani da na’ura.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel