A kalla mutane 70 sun hallaka sakamakon tashin wata gobara a gidan yari

A kalla mutane 70 sun hallaka sakamakon tashin wata gobara a gidan yari

A kalla mutane 70 ne rahotanni suka bayyana cewar sun hallaka a wata gobara da ta tashi a babban gidan dake yankin Valencia, a arewa da Carabobo, babban birnin kasar Venezuela, babban birnin jihar.

Rahotanni sun bayyana cewar gobarar ta tashi ne bayan da fursunonin suka tattara katifu sannan suka cinna masu wuta domin samun sararin guduwa daga gidan yarin.

Da yawan fursunoni sun mutu ne sakamakon samun kuna da kuma shakewar da hayaki ya yi masu.

Babban jami'in gidan yarin, William Saab, ya ce wani bincike na farko ya tabbatar da mutuwar mutane 66 maza da kuma mata biyu da suka kawo ziyara.

A kalla mutane 70 sun hallaka sakamakon tashin wata gobara a gidan yari

A kalla mutane 70 sun hallaka sakamakon tashin wata gobara a gidan yari

An samu tashin hatsaniya bayan zuwan 'yan sanda a yayin da suke kokarin hana jama'a cikin gidan yarin domin ceto 'yan uwansu.

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya ceci jam'iyyar APC - Shugaban jam'iyyar

Gwamnatin babban birnin kasar, Carabobo, ta kafa kwamitin jami'an ma'aikatar kula da gidajen yari domin gudanar da binciken kwakwaf a kan musabbabin tashin gobarar.

Gidajen dake kasashen kudancin Amurka na fama da matsanancin cunkuso da kuma karancin kudade.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel