Yadda Buhari ya ceci jam'iyyar APC - Shugaban jam'iyyar

Yadda Buhari ya ceci jam'iyyar APC - Shugaban jam'iyyar

Shugaban jam'iyyar APC a jihar Edo, Anslem Ojezua, ya bayyana cewar shugaba Buhari ya ceto jam'iyyar daga fadawa cikin hargitsi irin na siyasa.

Da yake ra'ayinsa a jiya a kan kin amincewar da Buhari ya yi da karin wa'adin ga shugabannin jam'iyyar na kasa, Ojezua, ya ce, shugaba Buhari ya kyauta matuka kuma ya kubutar da jam'iyyar daga shiga rigingimu masu alaka da kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

A cewar Ojezua, ba don Buhari ya dakatar da shawarar da majalisar zartarwa jam'iyyar suka dauka ba, to babu abinda zai hana jam'iyyar samu babbar tangarda.

Yadda Buhari ya ceci jam'iyyar APC - Shugaban jam'iyyar

Buhari da Oyegun

"Jawabin shugaba Buhari ya zo a daidai lokacin da ya dace saboda daya daga cikin abubuwan da jam'iyyar APC tayi alkawarin shine tabbatar da dimokradiyyar cikin gida," inji Ojezua.

Sannan ya cigaba da cewa, "jawabin shugaba Buhari ya tabbatar wa da 'yan Najeriya da duniya cewar akwai dimokradiyya a cikin jam'iyyar APC kuma hakan ya karawa jam'iyyar daraja da kima a idon mutane."

DUBA WANNAN: An kama matsafi da kayuwan mutane uku a Ilorin

Ojezua ya ce, matakin da shugaba Buhari ya dauka zai kara saka kaunar jam'iyyar APC a zukatan sabbin 'yan jam'iyyar kuma zai kara jawo ra'ayi ra'ayin jama'a su shigo jam'iyyar domin sun san zasu samu damar yin siyasa a cikin jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel