Babachir, Ajimobi, Ganduje, Tambuwal da sauran mutane sun halarci babban taron Tinubu

Babachir, Ajimobi, Ganduje, Tambuwal da sauran mutane sun halarci babban taron Tinubu

Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, tsohon sakataren gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki sun isa filin bababn taron Bola Tinubu na 10.

Tinubu, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Lagas kuma shugaban jam’iyyar APC ta kasa zai yi amfani da wannan zama domin murnar agayowar ranar haihuwarsa karo na 66.

Sauran manyan mutane da suka isa wajen taron sun hada da Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi, Oba na Lagas, Riliwanu Akiolu, Alake na Egbaland, Aremu Gbadebo.

Har ila yau tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, sanatoci da yan majalisa na zaune a wajen taron.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya bukaci magoya bayansa da suyi katin zabe kafin 2019

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Mista Perry Opara ciyaman na jam’iyyar NUP ya bayyana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin zakin siyasa,wanda yake taimakawa wurin samun nasara a zabe.

Opara yace, duk dan siyasa ko jam’iyyar da bata nemi shawarar Obasanjo ba a bangaren harkokin siyasa, tana cikin bata a zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel