Sanatocin jihar Kaduna sunyi wa El-Rufai kafar ungulu a kan ranto $350m

Sanatocin jihar Kaduna sunyi wa El-Rufai kafar ungulu a kan ranto $350m

Majalisar Dattawa ta ki amincewa da bukatar gwamnatin Jihar Kaduna na karbo bashin $350m bayan tattaunawa a kan batun har na tsawon shekara daya.

Kin amincewar Majalisar ya faru ne sakamakon yin la'akari da rahoton kwamitin majalisa na basuskan cikin gida da kasashen waje karkashin jagorancin Sanata Shehu Sani na jam'iyyyar APC daga jihar ta Kaduna.

Majalisa ta ki amincewa jihar Kaduna karbo bashin $350

Majalisa ta ki amincewa jihar Kaduna karbo bashin $350

Sanata Sani ya ce amincewa da karbo bashin zai rubanya adadin kudaden da ake bin jihar daga $232m zuwa $532. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu jihar Kaduna ce ta biyu a jerin jihohin da sukafi nauyin bashi a kasar nan.

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Botswana ya sauka daga mulki

Sanata Suleiman Othman Hunkuyi daga jihar Kaduna shima ya goyi bayan kun amincewa da bashin inda ya bayyana cewa ba abu ne mai muhimmanci ga jihar ba.

Hakazalika, Sanata Danjuma La'ah daga jam'iyyar PDP na jihar Kaduna shima ya tofa albarkacin bakinsa inda ya ce bai dace a bayar da umurnin ciyo bashin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel