Atiku ya bukaci magoya bayansa da suyi katin zabe kafin 2019

Atiku ya bukaci magoya bayansa da suyi katin zabe kafin 2019

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira ga magoya bayansa da suyi katin zabe kafin zaben 2019

- An fara rajistar katin zaben tun a watan Janairu na shekara 2018 kuma za’a gama a ranar 31 ga watan Maris

- Za’a cigaba da rajistar wadda aka fara tun shekarar 2017, har zuwa kwana 60 kafin ranar da za’a gudanar da babban zabe

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira ga magoya bayansa da suyi katin zabe kafin zaben 2019.

An fara rajistar katin zaben tun a watan Janairu na shekara 2018 kuma za’a gama a ranar 31 ga watan Maris.

Za’a cigaba da rajistar wadda aka fara tun shekarar 2017, har zuwa kwana 60 kafin ranar da za’a gudanar da babban zabe.

Atiku ya bukaci magoya bayansa da suyi katin zabe kafin 2019

Atiku ya bukaci magoya bayansa da suyi katin zabe kafin 2019

Tsohon mataimakin shugaban kasar yayi kiran ne lokacin da aka kaddamar da shafinsa na yanar gizo, na magoya bayansa (CC4ATIKU). Shafin shine www.cc4atiku.org

Tsohon Mataimakin shugaban kasar wanda ciyaman din kungiyar magoya bayan Atiku, Oladimeji Fabiyi, yace kimiyya zata bayar da gagarumar gudumuwa ta bangare zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Obasanjo ne uban siyasar Najeriya – Shugaban jam’iyyar NUP

Ya bayyana cewa zabe ba’a kafar yade labarai ake yinshi ba, dole masu zabe suyi rajista don zabar wanda suke so.

Ya bukaci matasan najeriya su shiga cikin siyasa domin su karba mulki daga hannun tsofaffin yan siyasa kamar yadda ya kafa kwamiti don yin haka.

Duk da cewa Atiku Abubakar bai fito fili ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa ba, yawancin mutane sunyi tunanin haka shiyasa yabar jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel