Da dumi-dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas

Da dumi-dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas

Bayan shekaru uku da nasarar zabe, shugaba Muhamadu Buhari ya isa jihar Legas domin ziyararsa na farko a yau Alhamis, 29 ga watan Maris, 2018.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyaran kwana 2 ne inda zai kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Legas ta aiwatar karkashin jagorancin gwamna Akinwumi Ambode.

Da dumi-dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas

Da dumi-dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas

Bayan kaddamar da ayyukan, shugaban kasan zai halarci taron lakcan bikin zagayowar ranan haihuwar babbanjigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Da dumi-dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas

Da dumi-dumi: Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Legas

KU KARANTA: Shugaban kasar Botswana ya sauka daga mulki

Mun kawo muku rahoton cewa ziyara da shugaban kasa zai kai jihar Legas a yau ta kawo takura ga matafiya a jirgin sama sakamakon rufe duka hanyoyin zuwa tashar

A yau safiyar alhamis ne aka rufe duk manyan hanyoyin zuwa tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed, a jihar Legas, sakamakon ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai a jihar.

Hakan ya sanya mutane cikin wahala, inda wasu na takawa kasa nisan kilo biyu, zuwa filin jirgin don su samu tafiya inda zasu.

Majiyarmu da ya ziyarci babban asibitin Ikeja a jihar, da misalin karfe 5 na asuba, ya tarar da jami’an tsaro da dama rike da makamai suna tsare da tashar mota na Olowu don tsaya don hana motoci safara a hanyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel