Nigerian news All categories All tags
Rashin tausayi: Wani mutum ya fille kan wata mata yayin da ta ke aiki a gonar ta

Rashin tausayi: Wani mutum ya fille kan wata mata yayin da ta ke aiki a gonar ta

- Hukumar ‘Yan Sanda ta kama wani mai suna Tochukwu Chianugo Idu, bisa ga zargin kashe wata mata kai tana aiki a gonarta

- Idu ya fille wa matar mai suna Susana Enejere kai lokacin da ya sameta tana aiki a cikin gonarta dake Ugbene

- Yanzu haka gawar marigayiyar na dakin aje gawa na kusa da kauyen, inda shi kuma wanda ake zargin yana hannun ‘Yan Sanda an gudanar da bincike

Hukumar ‘Yan Sanda ta kama wani mai suna Tochukwu Chianugo Idu, dan garin Ugwuoda Nimbo a karamar hukumar Uzo Uwani, bisa zargin hallaka wata mata mai suna Susana Enejere, ta hanyar fille mata kai a cikin gonarta, a Ugbene Ajima, a ranar 26 ga watan Maris. Hakan ya biyo bayan tafiyar Enejere gona bata dawo ba yasa danginta suka bazu nemanta.

Rashin tausayi: Wani mutum ya fille kan wata mata yayin da ta ke aiki a gonar ta

Rashin tausayi: Wani mutum ya fille kan wata mata yayin da ta ke aiki a gonar ta

KU KARANTA: APC za ta rushe kafin zaben 2019, inji wani tsohon dan takarar gwamna

Jami’in ‘Yan Sanda mai kula da hulda da jama'a, na jihar, Ebere Amariazu, wanda ya tabbatar da labarin a wata sanarwa a Enugu a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an kama mutumin ne ta hanyar rahoton da aka samu. inda ya kara da cewa Idu ya jagoranci ‘Yan Sanda zuwa inda ya binne marigayiyar, inda aka samu gangar jiki da kan marigayiyar da ya yanke.

An samu labarin cewa lokacin da bata dawo gida ba, wan shekare 27 ga watan Maris, 2018, aka bazu kan nemanta, inda sakamakon rohoton kwararru ya kaiga kamen Tochukwu Idu Chianugo dan kauyen Ugwuoda, a Nimbo, wanda ake zargi da hannu a kisan Enejere.

Bayan kamashi, ya jagoranci hukumar ‘Yan Sandan zuwa wurin da ya cirewa marigayiyar kai. Da gangar jikin da kan da aka cire an gansu kuma an kaisu dakin ajiyar gawa na asibiti a jihar, shi kuma wanda ake zargin yana hannun jami’an ‘Yan Sanda suna cigaba da bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel