Nigerian news All categories All tags
Zambar kudi N63m: 'Yan sanda na neman wasu ma'aurata ruwa a jallo

Zambar kudi N63m: 'Yan sanda na neman wasu ma'aurata ruwa a jallo

- Hukumar Yan sanda tana neman wasu ma'aurata ruwa a jallo bisa tuhumar su da damfara

- Ana zargin ma'auratan, Mrs Chinyere Amalunweze da mijinta Tony Amalunweze ta hadin baki da wasu a kamfanin wajen sace kudi N63m

- Hukumar Yan sandan na rokon al'umma duk wanda ya ke da wani bayyani game da su yayi gagawan sanar da ofishin yan sanda

Rundunar Yan sandan Najeriya reshen jihar Enugu ta bayar da sanarwan neman wasu ma'aurata ruwa a jallo bisa zargin su da aikata laifin damafara da zamba a wata kamfanin bayar da bashi kamar yadda kamfanin dillanci labarai (NAN) ta ruwaito.

Zambar kudi N63m: 'Yan sanda na neman wasu ma'aurata ruwa a jallo

Zambar kudi N63m: 'Yan sanda na neman wasu ma'aurata ruwa a jallo

A sanarwan ta ta fito ta bakin mai magana da yawun hukumar, SP Ebere Amaraizu a ranar Alhamis a garin Enugu, ya bayyana cewa sashin binciken masu aikata manyan laifuka na rundunar ta dukufa wajen gudanar da bincike a kan lamarin.

KU KARANTA: Faduwar jarabawar WAEC: Majalisa ta bukaci Ministan Ilimi ya bayyana a gaban ta

Amaraizu ya bayar da yayi kwatancen kamanin matar da mijin inda ya ce matar mai suna Mrs Chinyere Amalunweze mai shekaru 36 yar asalin kauyen Umuego Edo a garin Nnobi na karamar hukumar Idemili na kudu a jihar Anambra fara ce kuma tsohuwar ma'aikaciyar kamfanin bayar da bashin ne.

Shi kuma mijinta, Mr Tony Amalunweze mai shekaru 38 dan asalin kauyen Umulumgbe ne da ke karamar hukumar Udi na jihar Enugu baki ne kuma yana zaune a gida mai lamba 2a Layin Akpugo a Independence Layout a garin Enugu.

"Ana tuhumar su ne da hadin bakin cikin wata makirci da aka shirya inda aka damfari kamfanin bashi kudi har naira miliyan 63 sannan daga bisani suka tsere.

"Hukumar Yan sandan na rokon al'umma su taimaka da duk wani bayyani da zai taimaka a gano inda suke ta hanyar kai rahato zuwa ofishin yan sanda mafi kusa da kai.

"Tuni, rundunar ta bayar da izinin kamo su ruwa a jallo duk inda suke," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel