Nigerian news All categories All tags
Anyi cecekuce a zaman ganawa na shugabannin jam'iyyar APC

Anyi cecekuce a zaman ganawa na shugabannin jam'iyyar APC

An samu karin rahotanni kan abubuwan da suka wakana dangane da ganawar sirrance ta shugabannin jam'iyyar APC da ya gudana a ranar Talatar da ta gabata.

Rahotanni da suka bayyana a ranar yau Laraba sun bayyana cewa, kalaman shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin ganawar ta sirrance ya janyo cecekuce da tayar da jijiyoyin wuya a tsakankanin mambobi na shugabannin jam'iyyar.

Daya daga cikin shugabannin jam'iyyar da bai bukaci a bayyana sunan sa ba ya ruwaito cewa, hatgitsi da cecekuce ya yi kakagida yayin da mambobi na shugabannin jam'iyyar suka tsawatar da shugaba na majalisar wakilai, Alhassan Doguwa, kan cewa ba sai anyi wata muhawara ba tun dai har shugaban kasa ya riga da yanke shawara.

Anyi cecekuce a zaman ganawa na shugabannin jam'iyyar APC

Anyi cecekuce a zaman ganawa na shugabannin jam'iyyar APC

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wannan hargitsi da tayar da jijiyoyin wuya ya sanya dogaran shugaban kasa suka afko cikin farfajiyar wannan taro domin daukar matakan tsaro na kiyayewa.

KARANTA KUMA: Yadda igiyar leko ta yiwa karen sigari fintinkau ta fuskar illata dan Adam

A daidai wannan lokaci, shugaban jam'iyyar ya yi barazanar amfani da karfin iko na kujearar sa wajen ficewa daga dakin taron muddin mambobin ba su shiga taitayin su ba.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, akwai jerin sanatoci 42 dake goyon bayan shugaba Buhari kan sauya fasalin zabe na 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel