Ziyarar shugaban kasa Buhari jihar Legas ta kawo takura ga matafiya a jirgin sama

Ziyarar shugaban kasa Buhari jihar Legas ta kawo takura ga matafiya a jirgin sama

- Ziyara da shugaban kasa zai kai jihar Legas a yau ta kawo takura ga matafiya a jirgin sama sakamakon rufe duka hanyoyin zuwa tashar

- Hakan ya sanya mutane cikin wahala, inda wasu na takawa kasa zuwa filin jirgin don su samu tafiya inda zasu

- Wasu daga cikin mutanen gari sun nuna damuwarsu akan haka, inda suke ganin cewa wannan keta hakkin bil adama ne

A yau safiyar alhamis ne aka rufe duk manyan hanyoyin zuwa tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed, a jihar Legas, sakamakon ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai a jihar.

Hakan ya sanya mutane cikin wahala, inda wasu na takawa kasa nisan kilo biyu, zuwa filin jirgin don su samu tafiya inda zasu.

Majiyarmu da ya ziyarci babban asibitin Ikeja a jihar, da misalin karfe 5 na asuba, ya tarar da jami’an tsaro da dama rike da makamai suna tsare da tashar mota na Olowu don tsaya don hana motoci safara a hanyar.

A lokacin hada wannan rahoto sai da jami’inmu na Premium Times yayi tafiyar tsawon kilo 2.6. Bayan haka, ma’aikatan Sojin Najeriya sun karbe masa wayar salula, akan cewa saita goge hotunan data dauka na halin da ake ciki.

KU KARANTA KUMA: Ainihin alawus da ya kamata 'yan majalisa suka rika karba - Hukumar RMAFC

A filin tashar jirgin kuma wani ma’aikacin Dana mai suna Charles, ya bayyana cewa za’a tsayar da tashin duka jirage har zuwa karfe 12 na rana bayan shugaban kasa ya iso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel