Nigerian news All categories All tags
Oshiomole zai maye kujerar Odigie-Oyegun na ciyaman a APC

Oshiomole zai maye kujerar Odigie-Oyegun na ciyaman a APC

- Kamar yanda ake ta cece kuce akan kudirin Buhari game da zabe mai zuwa na 2019

- APC ta fadawa kotu cewa Shugaba Buhari bashi da hurumin da zai canzawa kwamitin zartarwa shawarar da suka yanke

- Oshiomole ake sa rai zai maye zauna kujerar Ciyaman na APC, Chief John Odigie-Oyegun

Comerade Adams Oshiomole, tsohon gwamna a jihar Edo, ake sa rai zai maye kujerar ciyaman na jam’iyyar APC, Chief Odigie-Oyegun.

Hakan ya biyo bayan kokarin da akeyi na sanya yankin nasu na kudu maso gabas cikin harkokin jagoranci a jam’iyyar.

A bayanin da jam’iyyar ta APC tayi a jiya, game da kudirin shugaba Buhari akan zabe, tace kudirin shugaban kasar bazai iya canzawa kwamitin zartarwa ta jam’iyya shawarar da suka yanke ba, sakamakon cewa shugaban kasar mutun daya ne da kuri’a daya.

Oshiomole zai maye kujerar Odigie-Oyegun na ciyaman a APC

Oshiomole zai maye kujerar Odigie-Oyegun na ciyaman a APC

Bayan haka, rashin canza shawara akan Karin wa’adi da aka yiwa shuwagabannin jam’iyyar yana ta kara kawo rudani a tsakanin ‘yan jam’iyyar gabanin zuwan zaben kasa baki daya, wanda hakan babbar matsalace ga jam’iyyar. Duk da cewa Oshiomole da Odigie tsofaffin gwamnoni ne, a jihar ta Edo.

Jaridar Vanguard a jiya ta ruwaito cewa, kasancewar Oshiomole a kan gaba cikin wadanda akesa ran bawa kujerar ciyaman din ya biyo bayan daidaituwarsu da Asiwaju Bola Tinubu, wanda shine shugaban jam’iyyar na kasa, kuma shine wanda ya fara nuna rashin yarda akan karawa Odiegie wa’adi.

KU KARANTA KUMA: Ku daina buga kwalayen siyasa da hotunan Buhari – BCO ta gargadi yan siyasa

Duk da cewa shekaru hudu da suka wuce ba shiri tsakanin Oshiomole da Tinubu, lokacin da Odiiegi ya zama ciyaman na jam’iyya.

Oshiomole na goyon bayan Tom Ikimi wanda yayi takarar ciyaman na jam’iyya tare da Odigie, inda Tinubu ya tsayawa Odigie, ya kuma tabbatar da ya samu wannan kujera.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel