Nigerian news All categories All tags
Oyegun ya kira taro ya daga bayan zaman sa a kujerar Shugaban Jam’iyya ya zo karshe

Oyegun ya kira taro ya daga bayan zaman sa a kujerar Shugaban Jam’iyya ya zo karshe

- APC ta kira taro ta kuma fasa yayin da Oyegun yake zama a kujera mai kafa daya

- An shirya zama da tsakanin manyan Jam’iyya da kuma ‘Yan Majalisa sai aka fasa

- Shugaban kasa Buhari ya nuna rashin goyon bayan sa da karin wa’adin Shugabanni

Mun samu labari daga Jaridar Punch cewa Shugaban Jam’iyyar APC John Odigie-Oyegun yayi kokarin kiran wani taro sai dai ya fasa bayan Shugaba Buhari ya nuna rashin amincewar sa da karin wa’adin da aka yi wa Shugabannin Jam’iyyar kwanaki.

Oyegun ya kira taro ya daga bayan zaman sa a kujerar Shugaban Jam’iyya ya zo karshe

Ba mamaki APC ta maye gurbin Oyegun da wani sabon Shugaba

John Oyegun ya fasa taron da ya shirya a jiya da ‘Yan Majalisa bayan zaman sa a kujerar ya kama hanyar zuwa karshe wanda hakan ya fusata jama’a da dama a Jam’iyyar. An kira taro ne na Majalisar NWC da kuma ‘Yan Majalisar kasar a jiya amma bai yiwu ba.

KU KARANTA: An fara shari'a tsakanin 'Ya 'yan APC a Kotu

Kamar yadda mu ka samu labari an shirya haduwar ne a wani dakin taro na Majalisar Wakilai na Tarayya inda har manyan ‘Yan Majalisar irin su Yakubu Dogara da Femi Gbajabiamila sun zauna sai su ka ji cewa zaman ba zai yiwu ba inda su ka tashi cikin fushi.

John Oyegun yayi niyyar ya tattauna wasu batutuwa ne da ‘Yan Majalisan kasar sai kuma labari ya canza. Honarabul Femi Gbajabiamila dai ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa har yanzu babu dalilin tada hankali don komai na tafiya dai-dai a Jam’iyyar ta su ta APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel