Nigerian news All categories All tags
Hukumar Kwastan sun lalata buhunhunan shinkafa a jihar Legas

Hukumar Kwastan sun lalata buhunhunan shinkafa a jihar Legas

- Hukumar kwastan ta lalata buhunhunan shinkafa dubu biyu daga cikin buhu dubu 12 data kama a watannin da suka gabata a iyakar Seme dake jihar Legas

- Bayan buhunhunan shinkafa da hukumar ta kwastan din ta kama, ta kuma kama motoci cike da atamfofi, duk da yake dai ba a haramta shigowa da atamfa ba amma tilas ne a biya mata kudin haraji

Hukumar Kwastan sun lalata buhunhunan shinkafa a jihar Legas

Hukumar Kwastan sun lalata buhunhunan shinkafa a jihar Legas

Hukumar kwastan ta lalata buhunhunan shinkafa dubu biyu daga cikin buhu dubu 12 data kama a watannin da suka gabata a iyakar Seme dake jihar Legas.

DUBA WANNAN: Ana cigaba da yiwa bakaken fata kisan gilla a kasar Amurka

Shugaban hukumar wanda yake kula iyakar kasa ta Seme dake yankin Badagry a jihar Legas, Kwanturola Muhammad Aliyu, ya bayyanawa manema labarai cewar ga wanda bai sani ba sai yaga kaman almubazzaranci ne hakan, amma shinkafar ta dade a ajiye har ya kai ga ta lalace.

A bayanin da yayi yace, idan suka kama shinkafa sai sun duba sun tabbatar da cewar mai kyau ce ko maras kyau, domin a ware su wuri daban-daban. Mai kyau din ita ce muke dauka muna kaiwa sansanin 'yan gudun hijira domin a taimaka musu. Maras kyau kuma sai mu tuntubi Abuja domin su bamu shawara akan yanda zamu yi da ita. Daga Abuja sai a kira hukumar kula da abinci da abin sha wato NAFDAC a takaice. Hukumar NAFDAC din tayi bincike ta bada sakamakon cewar ko dabba bai kamata a bata shinkafar ba balantana kuma mutum.

Mista Sunday Ona Oche Mataimakin Darakta na hukumar NAFDAC, shine yake taimakawa domin ganin an binne gurbataccen abinci, ko kuma abin sha, ko kwayoyi masu wadanda ba a aminta dasu ba. Mista Oche ya kara bayyana wa manema labarai cewar hukumar ta NAFDAC tare da hadin gwiwar hukumar Kwastan da kuma sauran hukumomi wadanda abin ya shafa dake yankin suna tafiyar da ayyukan su yanda ya kamata domin dakile shigowa da kaya wadanda gwamnati bata yadda dasu ba, musamman ma abinci ko kwayoyin magunguna wanda ba a aminta dasu ba.

Bayan buhunhunan shinkafa da hukumar ta kwastan din ta kama, ta kuma kama motoci cike da atamfofi, duk da yake dai ba a haramta shigowa da atamfa ba amma tilas ne a biya mata kudin haraji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel