Nigerian news All categories All tags
Ana cigaba da yiwa bakaken fata kisan gilla a kasar Amurka

Ana cigaba da yiwa bakaken fata kisan gilla a kasar Amurka

- A duk lokacin da gari ya waye a kasar Amurka hukumar 'yan sanda na kasar Amurka sai sun harbe bakar fata har lahira, amma har yanzu shugabannin kasar dake fadar White House basu dauki wani kwakkwaran mataki akan hakan ba, hasali ma sun nuna halin ko in kula akan lamarin

Ana cigaba da yiwa bakaken fata kisan gilla a kasar Amurka

Ana cigaba da yiwa bakaken fata kisan gilla a kasar Amurka

A duk lokacin da garin Allah ya waye a kasar Amurka hukumar 'yan sanda ta kasar Amurka sai sun harbe bakar fata har lahira, amma har yanzu shugabannin kasar dake fadar White House basu dauki wani kwakkwaran mataki akan hakan ba, hasali ma sun nuna halin ko in kula akan lamarin.

DUBA WANNAN: Burin wasu ma'aurata ya cika sun mutu a rana daya

A wannan satin ma wani jami'in dan sanda a yankin Houston na kasar ta Amurka, ya harbi wani dattijo mai shekaru 54 inda yayi sanadiyyar mutuwar shi. Jami'in dan sandan wanda yake kokarin raba wasu mutane da suke gardama akan titi, ya daga bindiga ya harbe wani bakar fata daga cikin masu gardamar har lahira.

A wani bidiyo da wasu shaidu suka dauka da wayar su ta salula, ya bayyana yadda mutumin ya gamu da ajalin sa babu gaira babu dalili. Bayan dan sandan ya harbe bakar fatar, dan sandan ya tsaya ya zuba wa mutumin ido yana ganin fitar ransa ba tare da ya nuna damuwar ya kashe rai ba.

Cece-kuce mai zafi ya kaure a shafin sada zumunta, a yayinda aka dora bidiyon a shafuka da dama na kafar sada zumuntar, inda mutane daga wurare daban-daban na duniya suka dinga tofin Allah tsine da yadda jami'an 'yan sanda suke cigaba da kashe bakar fata basu jiba basu gani ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel