Nigerian news All categories All tags
Yan Shia 10,000 sun mamaye majalisar dokoki, sunce a shirye suke su mutu domin El-Zakzaky

Yan Shia 10,000 sun mamaye majalisar dokoki, sunce a shirye suke su mutu domin El-Zakzaky

Kimanin mambobin kungiyar musulman Shia 10,00 ne suka mamaye a majalisar dokoki a ranar Laraba, 28 ga watan Maris domin yin zanga-zanga kan ci gaba da tsare shugabansu Sheikh El-Zakzaky da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ci gaba da yi.

Kungiyar sun nuna damuwa akan lafiyar El-Zakzaky inda suka bayyana cewa ya zama dole yan majalisa su umurci fadar shugaban kasa da ta sake shi ba tare da uzuri ba domin ya samu kulawar likita yadda ya kamata.

Da yake Magana a lokacin zanga-zangan, sakataren kungiyar, Abdullahi Ahmed Musa, yace mambobin kungiyar sun shirya mutuwa don tabbatar da cewa an saki El-Zakzaky daga tsaren da yake.

Yan Shia 10,000 sun mamaye majalisar dokoki, sunce a shirye suke su mutu domin El-Zakzaky

Yan Shia 10,000 sun mamaye majalisar dokoki, sunce a shirye suke su mutu domin El-Zakzaky

Ya kuma bayyana cewa kungiyar zata shirya mambobinta sama da miliyan 10 daga fadin kasar domin mamaye babban birnin tarayya.

KU KARANTA KUMA: A bayyana mana musabbabin rugujewar coci a 2016 – Wani Lauya ya fadawa Gwamna Udom

Yan Shi’an sun samu tarba daga Sanata Kabir Gaya a madadin shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki wanda yayi alkawarin tabbatar da cewa dukannin bangarori biyu na majalisar dokoki sun shirya kwamiti domin duba ga bukatarsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel