Nigerian news All categories All tags
APC za ta rushe kafin zaben 2019, inji wani tsohon dan takarar gwamna

APC za ta rushe kafin zaben 2019, inji wani tsohon dan takarar gwamna

- Tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP yace APC za ta rushe kafin zaben 2019

- Onuesoke yace jami’yyar ta APC za ta rushe ne sakamakon wahalhalu da matsi da ta jefa al'ummar Najeriya ciki

- Onuesoke yayi ikirarin cewa muddin jam’iyyar APC ta gudanar da taron kasa don zabar sababin shuwagabannin jam’iyyar za ta rikice

Tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP na jihar Delta, yayi hasashen cewa jam’iyyar APC za ta rushe kafin zaben 2019, hakan ya biyo bayan ‘yan matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta game da shuwagabannin da ke jagorancinta da kuma wahalar da mutanen kasa ke fuskanta na rayuwa.

APC zata tarwatse kafin 2019 - Jam'iyyar PDP

APC zata tarwatse kafin 2019 - Jam'iyyar PDP

Wannan ya kasance a cikin wata sanarwa da tsohon dan takarar gwamnan ya bayar a ranar Laraba yayin da yake mayar da martani a kan maganar da Ministan Harkokin Labarai da Al’adu , Alhaji Lai Mohammed yayi na hana jam’iyyar PDP rajista.

DUBA WANNAN: Sauya jadawalin zabe: An bayyana sunayen ‘yan Majilasar Dattawa masu goyon bayan Buhari

Onuesoke ya kalubalanci jam’iyyar adawa da su gudanar gudanar da taron kasa don zabar sababin shuwagabannin jam’iyya, su gani idan jam’iyyar bata rikice ba. Ya kuma bayyana cewa tun lokacin da suka karbi mulki a shekarar 2015, suna ta kokarin hada kan jam’iyyar su ta hanyar ba ta sunayen sauran jam’iyyu.

A mulkin da su kayi na shekaru uku yanzu, babu wani cigaba da suka kawo a kasar, dole kayi tunanin dame zasuyi amfani suyi kamfe a zaben 2019, shiyasa suke so a hana jam’iyyar PDP rajista, yanda za suyi zabe ba abokan takara, dama wannan shine dabarar su tunda mutane yanzu sun daina yarda dasu”, inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel