Zamu kama duk wanda ya yi zanga-zanga ko bore yayin ziyarar Buhari - Kwamishinan 'yan sandan Legas

Zamu kama duk wanda ya yi zanga-zanga ko bore yayin ziyarar Buhari - Kwamishinan 'yan sandan Legas

Kwamishinan 'yan sandan a jihar Legas, Edgal Imohimi, ya ce zasu kama duk 'ya'an kungiyar lauyoyin muddin suka gudanar da zanga-zanga yayin ziyarar shugaba Buhari zai kai jihar a yau.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta bakin kakakinta na jihar Legas, SP Chike Oti, ta ce, hankalin hukumar ya kai kan wani rahoto da aka alakanta da shugaban kungiyar lauyoyi reshen Ikeja dake nuna cewar 'yan kungiyar zasu gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da wata doka a mallakar kasa da jihar Legas ta zartar.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce, ya tabbatar da cewar masu neman rudani ne ke son yin amfani da kungiyar domin kawo tsaiko ga al'amura yayin ziyarar shugaba Buhari.

Zamu kama duk wanda ya yi zanga-zanga ko bore yayin ziyarar Buhari - Kwamishinan 'yan sandan Legas

Kwamishinan 'yan sandan Legas; Edgal Imohimi

Imohimi ya ce, "na san jama'a ba zasu manta cewar, hukumar 'yan sanda ta bayar da tsaro ga kungiyar lauyoyi reshen Ikeja ranar 12 ga watan Maris, 2018, yayin zanga-zangar nuna kin amincewa da sabuwar dokar mallakar kasa a jihar Legas. Har gidan gwamnatin jiha muka raka su kuma muka rako su suka dawo gida bayan kammala zanga-zangar."

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kwace makamai 198 daga daga hannun makiyaya da barayin shanu a jihar Katsina

Imohimi ya cigaba da cewa, "Abin bacin rai ne yanzu kungiyar ta ce zata kara yin wata zanga-zangar yayin ziyarar shugaban kasa. Hukumar 'yan sanda ba zata yarda da hakan ba kuma muna kira ga 'ya'yan kungiyar da su jingine batun zanga-zangar ko su gamu da fushin hukuma."

A yau ne ake saka ran shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kai ziyarar aiki jihar Legas domin kaddamar da wasu aiyuka da gwamnatin jihar ta yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel