Aiki ya kwana: Wani ma’aikacin NEPA ya gamu da ajalinsa a saman falwaya

Aiki ya kwana: Wani ma’aikacin NEPA ya gamu da ajalinsa a saman falwaya

Wanda bai ji bari ba, tabbasa zai ji hoho, inji malam bahaushe, kwatankwacin lamarin da ya faru kenan a jihar Kaduna, inda wani mutumi mai suna Ewuga da yayi dare dare a saman falwaya ya fado ya mutu.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Takata 27 ga watan Maris, a unguwar bayan Loco dake garin Kafanchan a karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna, inda Ewuga ya hau kan falwaya da nufin mayar da wayoyin wutar da kamfanin wuta suka yanke masa, sakamakon rashin biyan kudin wuta.

KU KARANTA: Yadda wani karamin Yaro ya tsallake rijiya da baya a hannun masu yankan kai a birnin Kebbi

Daily Trust ta ruwaito Ewuga, wanda ma’aikacin wucin gadi ne da hukumar lantarkin ta KAEDCO, yayi nasarar mayar da wayoyin wutar, amma sai zuma suka taso masa, inda a garin ya kauce ma zumar ne, sai ya tabo wayar wutar, nan take ya mutu.

Aiki ya kwana: Wani ma’aikacin NEPA ya gamu da ajalinsa a saman falwaya

ma’aikacin NEPA

Majiyar Legit.ng ta ji ta bakin wani dan unguwar, wanda yace: “A kokarinsa na kauce ma zumar ne ya taba wata wayar wuta, nan take ya fadi matacce tun kafin a kai masa agaji”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel