Nigerian news All categories All tags
A bayyana mana musabbabin rugujewar coci a 2016 – Wani Lauya ya fadawa Gwamna Udom

A bayyana mana musabbabin rugujewar coci a 2016 – Wani Lauya ya fadawa Gwamna Udom

- Wani babban Lauya ya shigar da Gwamna Emmanuel Udom kara a Kotu

- Shekarun baya wani coci ya ruguje a Jihar Akwa Ibom aka kuma rasa rai

- Lauyan dai ya nemi a bayyanawa Jama’a abin da ya jawo wannan hadari

Wani Lauya da ke Garin Legas Inibehe Effiong ya maka mai girma Gwamnan Jihar Akwa Ibom Emmanuel Udom da kuma Kwamishinan shari’ar sa a gaban Kotu game da wani hadari da ya auku kwanakin baya a Jihar ta Akwa Ibom.

A bayyana mana musabbabin rugujewar coci a 2016 – Wani Lauya ya fadawa Gwamna Udom

An shigar da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom Emmanuel Udom kara a Kotu

A bara wancan an samu wani hadari a Garin Uyo inda wani coci ya ruguje ana tsakiyar ibada. Gwamnatin Jihar ta sa ayi bincike tun tuni game da lamarin amma har yanzu ba a bayyana abin da aka gano a binciken da aka gudanar ba.

KU KARANTA: Ba a gama da 'Yan Boko Haram ba har yanzu - Fasehun

A Ranar Talatar nan ne babban Lauya Inibehe Effiong ya nemi Kotu ta tursasa Gwamnatin Jihar ta fito da sakamakon binciken da tayi a fili. Effiong ya nemi Kwamishinan shari’a ya ba shi takardar binciken da aka gabatar ya gani.

Wannan mummunan hadari dai ya faru ne a karshen 2016 inda mutane akalla 27 su ka rasu. Gwamnan ya nada kwamiti na mutum 8 karkashin wani tsohon Alkali Umoekoyo Essang su yi bincike kan musabbabin hadarin amma shiru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel