Ai ga irin ta nan: Sanatan da ya tsayawa Nnamdi Kanu a Kotu zai shiga gidan yari

Ai ga irin ta nan: Sanatan da ya tsayawa Nnamdi Kanu a Kotu zai shiga gidan yari

- Sanatan Najeriya da ya sa hannu aka bada belin Kanu ya shiga uku

- Jagoran Kungiyar IPOB ta Biyafara Nnamdi Kanu dai ya tsere yanzu

- Kotu tace ayi maza a fito da Nnamdi Kanu ko kuma a yabawa aya zaki

Ba mamaki Sanata Enyinnaya Abaribe na Jihar Abia da wasun su za su yabawa aya zaki bayan da Kotun kasar tayi barazanar daure Sanatan na Najeriyan da ya sa hannun sa aka bada belin Jagoran Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu.

Ai ga irin ta nan: Sanatan da ya tsayawa Nnamdi Kanu aK otu zai shiga gidan yari

Kotu tace Sanata Enyinnaya Abaribe yayi kashin Kanu

Kwanakin baya can Enyinnaya Abaribe sa wasu ne su ka tsayawa Nnamdi Kanu aka bada belin sa. Sai dai bayan sabawa dokokin belin, yanzu haka ma ba a san inda Nnamdi Kanu ya shige ba don haka aka ce za sun nemo shi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi ta'adi a Jihar Zamfara kwanan nan

Alkali mai shari'a a babban Kotun Tarayya ta Abuja Binta Nyako tace Sanatan da kuma wani Limamin Yahudu Immanuel El-Shalom da kuma wani Bawan Allah Tochukwu Uchendu su san yadda za su yi su fito da Nnamdi Kanu.

Kotu tace idan ba su fito da Kanu ba to za su iya asarar kudin jinginar da su ka ajiye har Naira Miliyan 100 da kuma yiwuwar shiga gidan kurkuku. Yanzu dai an rasa inda Nnamdi Kanu ya shige tun bayan da Sojoji sun ka shiga gidan sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel