Nigerian news All categories All tags
Hukumar da ke gindaya albashi ta fadi alawus din ‘Yan Majalisa

Hukumar da ke gindaya albashi ta fadi alawus din ‘Yan Majalisa

Hukumar RMAFC wanda ke tsaga albashin Ma’aikatan Gwamnati ta bayyana alawus din da kowane ‘Dan Majalisar Dattawa yake karba a wata bayan takaddamar da aka yi tayi a baya.

A kowane wata Sanatan Najeriya na tashi da Miliyan 1.6 a matsayin alawus din sa ne kurum inji Hukumar. Wannan dai ta sabawa batun da aka sani na cewa ‘Yan Majalisar na karbar abin da ya haura Naira Miliyan 13 a matsayin alawus.

Hukumar da ke gindaya albashi ta fadi alawus din ‘Yan Majalisa

RMFAC ta fadi alawus din ‘Yan Majalisar Dattawa

Hukumar ta bayyana cewa Shugabannin Majalisa ne kadai za su iya yi wa ‘Yan Najeriya bayanin inda kowane Sanata yake samun wadannan makudan Miliyoyi. Mai magana da bakin Hukumar Ibrahim Mohammed yayi wannan jawabi.

KU KARANTA: Majalisa ta musanya zargin karbar cin hanci

Kowane Sanatan kasar na samun N168,866:70 a matsayin alawus din fetur din mota da kuma wasu N126,650:00 na biyan ma’aikata. Bayan nan akwai kudi da ake warewa domin Hadimai da kuma tufafi da jarida da gidan haya da sauran su.

Ga dai jerin alawus din na a kasa:

Mota - N126,650:00

Albashin Hadimai - N42,216:66

Ma’aikatan gida -126,650:00.

Shakatawa-N50,660:00.

Yau da kullum - N50,660:00.

Kudin Jarida - N25,330:00.

Kudin tufafi -N42,216:66.

Gida-N8,443.33:00.

Kudin gunduma -N422,166:66

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel