Nigerian news All categories All tags
Jihar Benuwe: Cacar baki yasa tayi wa saurayinta yankan rago

Jihar Benuwe: Cacar baki yasa tayi wa saurayinta yankan rago

- Wata budurwa da aka bayyana sunanta da Sandra Doo a kafar sadarwa ta Facebook, ana zargin ta da yiwa saurayinta mai suna Lekke Terkaa, yankan rago a jihar Benue a yayinda cacar baki ta hada su

- Winnie, kanwa ce a wurin marigayin ta rubuta yanda lamarin ya faru da yayan nata tare da budurwar tasa a shafin ta na Facebook, inda ta ce wacce ake zargin ta yanka saurayin nata, sannan ta tsaya akan shi har sai data tabbatar da cewar baya motsi sannan ta tafi ta kyale shi

Jihar Benuwe: Cacar baki yasa tayi wa saurayinta yankan rago

Jihar Benuwe: Cacar baki yasa tayi wa saurayinta yankan rago

Wata budurwa da aka bayyana sunanta da Sandra Doo a kafar sadarwa ta Facebook, ana zargin ta da yiwa saurayinta mai suna Lekke Terkaa, yankan rago a jihar Benue a yayinda cacar baki ta hada su.

DUBA WANNAN: Boko Halas: Budurwa da ta hada digiri na ukku a Arewa maso Gabas ko shekaru 35 bata kai ba

Winnie, kanwa ce a wurin marigayin ta rubuta yanda lamarin ya faru da yayan nata tare da budurwar tasa a shafin ta na Facebook, inda ta ce wacce ake zargin ta yanka saurayin nata, sannan ta tsaya akan shi har sai data tabbatar da cewar baya motsi sannan ta tafi ta kyale shi.

Ga abinda Winnie ta rubuta a shafin ta na Facebook:

Dan Allah jama'a ayi hankali da wannan shaidaniyar matar, ta cakawa dan uwana wuka sai da ya mutu har lahira tana tsaye tana kallon shi. Sannan kuma a dinga lura da wadanda kuke soyayya dasu a wannan lokacin saboda ba kowacce ke da halayen kirki ba.

Ina rokon Allah ya saka mana, sannan kuma ya daukar mana fansa akan wannan azzalumar matar, da ace ina iko ko doka a hannuna na tabbata da wannan matar baza ta kara minti daya a duniya ba. Bani da karfi ko ikon yin wani abu yanzu, amma na tabbata Allah ba zai barki haka ba.

A lura dakyau dan Allah sunanta (Sandra Doo) a Facebook, sannan ina rokon jama'a da a cigaba da yada wannan labarin har sai kowa yasan halayenta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel