Nigerian news All categories All tags
Sauya Fasalin Zaben 2019: Sanatoci 42 na goyon bayan shugaba Buhari

Sauya Fasalin Zaben 2019: Sanatoci 42 na goyon bayan shugaba Buhari

Da sanadin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, akwai jerin sanatoci 42 dake goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari akan rashin sauya fasalin zaben kasa na 2019 da majalisar dattawa ta huro wuta don ganin ta sauya.

Wannan lamari ya sanya majalisar da rabu gida biyu, inda tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ya jagoranci sanatocin da suka dafa baya ga shugaban kasa Buhari.

Farfajiyar Majalisar Dattawa

Farfajiyar Majalisar Dattawa

Kadan daga cikin sunayen sanatoci masu goyon bayan shugaba Buhari sun hadar da; Ali Ndume, Ahmad Lawan, Jibrin Barau, Ovie Oma-Agege, Abdullahi Adamu, Abu Ibrahim da Tayo Alasoadura.

KARANTA KUMA: Jihohi 10 mafi tsala-tsalan mata a Najeriya

Legit.ng ta kawo muku jerin matsaya ta sanatocin kowace jiha dake goyon bayan shugaba Buhari:

Abia - 0

Adamawa - 3

Anambra - 1

Akwa Ibom - 1

Bauchi - 0

Benuwe - 1

Borno - 1

Bayelsa - 0

Cross River - 1

Delta - 0

Ebonyi - 1

Edo - 1

Enugu - 0

Ekiti - 0

Abuja - 0

Gombe - 0

Imo - 2

Jigawa - 2

Kaduna - 1

Kano - 2

Katsina - 3

Kebbi - 1

Kogi - 0

Kwara - 0

Legas - 3

Nasarawa - 1

Neja - 1

Ondo - 3

Osun - 2

Oyo - 2

Ogun - 2

Filato - 2

Ribas - 2

Sakkwato - 0

Taraba - 1

Yobe - 2

Zamfara - 0

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma lauyan kolu na kasa, Abubakar Malami, sun ki amincewa da wannan tsari na sauya fasalin zaben domin kundin ya bayar da dama ga hukumar zabe ta kasa watau INEC ta yi ruwa da tsaki a duk al'amurran zabe.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wata mata a kasar Saudiyya ta shafe shekaru 25 tana jinyar mijinta ba tare da kosawa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel