‘Yan Najeriya bazuyi dana sanin dora Buhari a kan mulki ba – Fadar shugaban kasa

‘Yan Najeriya bazuyi dana sanin dora Buhari a kan mulki ba – Fadar shugaban kasa

- ‘Yan Najeriya sun dage akan ganin sun dora shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki a zaben 28 ga watan Maris, 2015

- Gashi yanzu shekara uku har ta wuce, amma ‘yan Najeriya basuyi dana sani ba akan wannan zabin da sukayi ba

- Hakan na nuna cewa shugaban kasar zai sake komawa kan kujerarsa in har ya nemi hakan a zaben, 2019 mai zuwa

A ranar Laraba 28 ga watan Maris ne ya cika shekara uku da zabar Buhari a matsayin shugaban kasa a lokacin da suka shiga matsatsi da halin kaka nikayi, suke bukatar ganin canji a mulkin kasa.

Buhari yayi nasarar doke dan takarar PDP wanda jam’iyyarsu ta share shekaru 16 tana mulkin kasar.

Gashi yanzu shekara uku har ta wuce, amma ‘yan Najeriya basuyi dana sani ba akan wannan zabin da sukayi ba, na zabar shugaba Muhammadu Buhari. jawabin ya fitone daga Ofishin shugaban kasa.

Hakan na nuna cewa shugaban kasar zai sake komawa kan kujerarsa in har ya nemi hakan a zaben, 2019.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda ya karbi cin hanci domin canja tsarin zabe – Majalisar wakilai

Bayan haka, kungiyoyi da dama sunyi kira ga shugaba Muhammadu Buhari daya sake tsayawa takarar shugaban kasa.

Legit.ng ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan jihar Abia, Orji Kalu, ya bayyana cewa jam’iyyar APC zata tursasa Buhari akan ya sake tsayawa takara a shekarar 2019.

Kalu yace, Buhari zai sake tsayawa takara idan ma yaki, jam’iyya zata sanyashi dole ya tsaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel