Nigerian news All categories All tags
Yanzu-yanzu: Sifeton yan sanda ya salami kwamishanan yan sandan jihar Kogi kan arcewan yan binidga daga kurkuku

Yanzu-yanzu: Sifeton yan sanda ya salami kwamishanan yan sandan jihar Kogi kan arcewan yan binidga daga kurkuku

Sifeto Janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, ya bada umurnin sallamar kwamishanan yan sandan jihar Kogi, Ali Janga, a yau Laraba 28 ga watan Maris, 2018.

An sallamu Ali Janga ne tare wasu manyan hafsoshin yan sana da ke aiki karkashinsa kan rawan da suka taka wajen tserewan wasu yan bindigan da ke yiwa sanata Dino Melaye aiki daga kurkukun yan sanda a jihar.

Yanzu-yanzu: Sifeton yan sanda ya salami kwamishanan yan sandan jihar Kogi kan arcewan yan binidga daga kurkuku

Yanzu-yanzu: Sifeton yan sanda ya salami kwamishanan yan sandan jihar Kogi kan arcewan yan binidga daga kurkuku

Yan bindigan wadanda suka bayyana cewa Sanata Dino Melaye ne mai daukan nauyins ta hanyar basu kudi da makamai sun tsere da safyar yau Laraba, gab da su bayyana a gaban babban kotun tarayya da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

KU KARANTA: Muna neman Dino Melaye ruwa a jallo - Hukumar Yan Sanda

Sifeton yan sandan ya umurci CP Esa Sunday Ogbu, kwamishanan ayyukan tarayya na shelkwatan yan sanda ya maye gurbinsa da wuri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel