Yiwa 'yan Boko Haram afuwa ya nuna cewa ba'a ci gallabar su ba - Fasehun

Yiwa 'yan Boko Haram afuwa ya nuna cewa ba'a ci gallabar su ba - Fasehun

Wanda ya kafa kungiyar kabilar Yarabawa 'Oduduwa Peoples Congress' Dacta Fredrick Fasehun ya Allah-wadai da afuwar da gwamnatin tarayya za tayi wa yan kungiyar Boko Haram.

A wata sanarwa da ya bayar yau Laraba, Fasehun ya ce afuwar babban alama ce da ke nuna ikirarin da gwamnati tarayya tayi na cin galabar kungiyar ba komi bane face farfaganda.

Yiwa 'yan Boko Haram afuwa ya nuna cewa ba'a ci gallabar su ba - Fasehun

Yiwa 'yan Boko Haram afuwa ya nuna cewa ba'a ci gallabar su ba - Fasehun

"Yin afuwa ga kungiyar ta'addan da tayi kaurin suna a duniya babban alama ce da ke nuna cewa gwamnati karya da farfaganda ta rika yiwa al'umma lokacin da tace an ci galaban Boko Haram," inji shi.

KU KARANTA: Dan hayar da ya kashe sannan ya binne maigidansa ya ce, ya yi nadama

A cewar Fasehun, afuwar da shugaba Muhammadu Buhari zaiyi ga yan kungiyar na Boko Haram cin fuska ne ga wadanda suka mutu, (Sojoji da farar hula), wadanda suka jikatta da kuma wanda suka rasa muhallinsu sakamakon ta'addancin da yan kungiyar suka rika aikatawa.

Ya kara da cewa "Idan dai gwamnatin ta ci gallaban yan kungiyar na Boko Haram toh babu wani dalili dai zai sa ayi musu afuwa. Abin da ya dace shine gwamnatin ta mayar da hankali wajen ragargazar burbushin yan kungiyar kamar yadda Iraqi tayi wa ISIS.

"Muna kira da gwamnati ta zartar da hukunci a kan yan kungiyar."

Ya kuma ce maimakon a kai su kotun da ake kai sauran al'umma, dace wa yayi a kai su kotunan sojoji kuma duk wadanda aka samu da laifi a yanke musu hukuncin kisa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel