Nigerian news All categories All tags
‘Yan Sanda Sun tabbatar da guduwar wadanda ake zargi Melaye ke basu makamai

‘Yan Sanda Sun tabbatar da guduwar wadanda ake zargi Melaye ke basu makamai

- Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kogi, Ali Janga, ya tabbatar da guduwar wadanda ake zargi da cewa Melaye ya basu makamai don tayar da hankali a jihar

- Janga ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun gudune daga hannun hukumar ‘Yan Sandan ta ‘A’ division, a garin Lokoja

- CP Janga, ya bayyana cewa, jami’an ‘Yan Sanda 13 dake kan aiki, a lokacin da wadanda ake zargin suka gudu an tsaresu don a bincikesu

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kogi, Ali Janga, a ranar Laraba, ya tabbatar da guduwar wadanda ake zargi su biyu, da cewa Sanata Dino Melaye ya basu makamai don tayar da hankali a jihar, kafin zuwan zaben 2019, sun gudu daga hannun hukumar ‘yan Sanda tare da wasu masu laifi su hudu.

Janga ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun gudune daga hannun hukumar ‘Yan Sandan ta ‘A’ division, a garin Lokoja, da misalign karfe 3:20 na dare, a ranar Laraba.

‘Yan Sanda Sun tabbatar da guduwar wadanda ake zargi Melaye ke basu makamai

‘Yan Sanda Sun tabbatar da guduwar wadanda ake zargi Melaye ke basu makamai

Wanda ake zargin sune Kabiru Seidu wanda ake kira Osama, sai Nuhu Salisu wanda ake kira da Small. Sauran wadanda suka gudu sune Aliyu Isa, Adams Suleiman, Emmanuel Audu, da kuma Musa Mohammed.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta mayar da Tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a tsarin makarantu

CP Janga, ya bayyana cewa, jami’an ‘Yan Sanda 13 dake kan aiki, a lokacin da wadanda ake zargin suka gudu an tsaresu don a bincikesu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel